6 Disamba 2021 - 14:37
​Siriya: An Kai Hare-Hare Kan Sansanonin Sojojin Amurka A Kasar

An kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka ‘yan mamaya guda biyu a kasar Siriya da kuma kan ayarin sojojin Amurka a kasar Irraki wadanda suke makobtaka da juna.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Tashar talabijin ta Presstv a nan birnin Tehran ta bayyana cewa hakan na faruwa ne a dai-dai lokacinda mutanen wadannan kasashe biyu suke kara nuna kiyayyarsu da ci gaba da mamayar kasarsu wanda sojojin Amurkan suke yi.

Labarin ya nakalto kakafen yada labarai na gwamnatin kasar Siriya sun ce an ji karar tashin boma-bomai a kan iyakar kasar Siriya da Iraki da kuma kan iyakar kasar da Jordan a ranar yau Lahadin.

Kamfanin dillancin labaran Saberoon News na telegrame ya tabbatar da labarin, amma bai bayyana irin asarorin da hare-haren suka haddasa ba. Wannan ba shi ne karon farko wanda mayakan Hashdushabi na kasar Iraki suke kaiwa ayarin sojojin Amurka hare-hare a kasar ta Iraki ba.

342/